Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Shugaban jihar arewa maso gabashin Somaliya, Abdul Qadir Ahmed (wanda aka fi sani da Ali Fardeh), ya ce "Isra'ila" ta san cewa amincewarta ga yankin "Somaliland" mai neman ballewa ba zai isa ya mayar da shi kasa da ke samun amincewar kasa da kasa mai yawa ba, yana mai la'akari da cewa matakin Isra'ila ya dogara ne akan muradun tsaro da geopolitical a kahon Afirka da Bahar Maliya.
Fardeh ya bayyana cewa "Tel Aviv ba ta yi amincewa da nufin bai wa hukumomin Hargeisa cikakken iko ba, sai dai don ƙarfafa tasirinta kusa da Tekun Aden da mashigar Babal-Mandab ne" wadda ke daya daga cikin muhimman hanyoyin ruwa na kasuwancin duniya da samar da makamashi.
Muradun Da Suka Wuce Amincewar Siyasa
Wannan jami'in Somaliya ya yi imanin cewa muhimmancin "Somaliland" ga "Isra'ila" ya samo asali ne daga yanayin wurinta da ke fuskantar gabar tekun Yemen kuma a kofar kudancin Bahar Maliya. Ya ce Isra'ila tana mai da hankali sosai ga Bahar Maliya bayan sauye-sauyen tsaro da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma tana neman samun wurin da zai ba ta damar yin tasiri a zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma lura da barazana masu zuwa daga Yemen.
Fardeh ya kara da cewa Somaliya da Yemen suna wakiltar yankuna biyu masu mahimmanci a lissafin Isra'ila, yana mai tabbatar da cewa "Tel Aviv ba ta zo don bai wa masu neman ballewa cikakken iko ba, sai don cimma muradunta na kanta." Ya yi imanin cewa "Isra'ila" tana kallon kahon Afirka da Tekun Aden a matsayin hanyar shiga don ƙarfafa tasirinta a yankin da kuma yin tasiri ga ƙasashe masu muhimmanci da ke fuskantar Bahar Maliya, ciki har da Masar da Saudiya.
A ranar 26 ga Disamba 2025, "Isra'ila" ta sanar da amincewarta a hukumance ga "Somaliland" a matsayin kasa mai cin gashin kanta. A gefe guda, gwamnatin Somaliya ta ƙi shawarar Isra'ila, kuma ta bayyana ta a matsayin "matakin da bai dace da doka ba da kuma cin zarafin ikon" ƙasar da haɗin kanta da iyakokinta da duniya ta amince da su.
Babal-Mandab A Tsakiyar Lissafi
Yankin "Somaliland" yana kan gabar kudancin Tekun Aden, yana fuskantar Yemen kuma kusa da mashigar Babal-Mandab, wadda jiragen ruwa ke wucewa tsakanin Tekun Indiya da Bahar Maliya da mashigar Suez.
Majalisar Zaman Lafiya da Tsaro ta Tarayyar Afirka ta yi nuni da cewa amincewar Isra'ila ta zo ne a daidai lokacin da fafatawar geopolitical ke ƙaruwa a gabar Bahar Maliya, kuma wurin da yankin yake na iya ba wa "Isra'ila" matattarar da ke fuskantar gabar Yemen don ayyukan lura da ruwa, leken asiri, da tsaro.
Sha'awar wuraren tashar jiragen ruwa da filin jirgin sama na Berbera ta ƙaru a cikin watannin baya-bayan nan. Jaridar "Le Monde" ta Faransa ta ambata cewa ana gudanar da ayyukan faɗaɗawa a kewayen filin jirgin sama na Berbera, yayin da hasashen tsaro ke nuna cewa za a iya amfani da wurin a nan gaba daga UAE, Amurka, da "Isra'ila."
Tawagar Amurka A "Somaliland"
Shugaban "Somaliland," Abdirahman Mohamed, ya gana da kwamandan sojojin Amurka na musamman a Afirka, Claude Tudor, a wata ganawa da aka bayyana a matsayin "muhimmiyar dabara."
Dangane da sanarwar fadar shugabancin "Somaliland," ganawar ta hada da "tattaunawa mai zurfi game da hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da muradun dabara tsakanin Jamhuriyar Somaliland da Amurka, musamman game da tsaron Bahar Maliya da Tekun Aden, da ƙarfafa tsaro da kwanciyar hankali a yankin kahon Afirka." Ko da babu tsaron Oho!!!
A nasa bangaren, Tudor ya ce "Amurka da Somaliland suna da muradun tsaro masu muhimmanci a ƙasa da teku," yana mai nuni da cewa "kwanciyar hankali a yankin kahon Afirka da tsaron hanyoyin ruwa na duniya suna da fifiko na dabara ga bangarorin biyu."
Ya kara da cewa Amurka a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da "Somaliland" a batutuwan dabara masu amfani ga bangarorin biyu, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da musayar bayanai da ƙwarewa da haɓaka haɗin gwiwar tsaro a mataki na gaba.
………………
Ra'ayinka